26 Agusta 2019 - 08:36
Muhammad Jawad Zarif; Muna Da Jan Aiki A Gabanmu

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif wanda yake halartar taron kungiyar kasashe masu karfin masana’antu a kasar Faransa, ya bayyana cewa; Hanyar da take gabanmu tana da wahala, amma ta cancanci mu kwatanta tafiya a kanta.

(ABNA24.com) Ministan harkokin wajen kasar Iran, Muhammad Jawad Zarif wanda yake halartar taron kungiyar kasashe masu karfin masana’antu a kasar Faransa, ya bayyana cewa; Hanyar da take gabanmu tana da wahala, amma ta cancanci mu kwatanta tafiya a kanta.

Zarif wanda ya yi rubutu a shafinsa na Twitter ya kara da cewa; A bayan fagen taron kungiyoyi masu karfin masana’antu, na yi ganawa mai tsawo da ministan harkokin wajen Faransa John Lodrian da kuma ministan kudi na Faransan, na kuma gana da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, bayan nan kuma na gana da wakilan Birtaniya da kuma Jamus.”

Zarif ya ci gaba da cewa; Hanyar da take gabanmu tana da tsawo,amma ta cancanci mu bi ta.”

A jiya Lahadi ne ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya ziyarci Faransa domin tattaunawa da shugabannin kasar Faransa.



/129